MAI AZUMIN NAFILA ZAI IYA KARYA AZUMINSA DA GANGAN

236

MAI AZUMIN NAFILA ZAI IYA KARYA AZUMINSA DA GANGAN ! !

Tambaya:

Aslm Na wayi gari da azumi sai aka kawo abinci sai na fasa azumin naci abincin ,malam yin hakan akwai laifi na sharia?

Amsa:

Wa alaikum assalam, ya halatta abin da ka yi, saboda fadin Annabi (s.a.w) “Mai azumin nafila sarkin kansa ne, in ya so ya cigaba da azumi, in ya so kuma ya karya”.
kamar yadda Tirmizi ya rawaito
Allah ne mafi sani.

Dr Jamilu Zarewa. 25/7/2016

Comments are closed.