Mahara sun saki ‘yan agaji 20 da suka yi garkuwa da a Zamfara

357

Idan ba a manta ba a watan Disamba ne masu garkuwa sun yi garkuwa da wasu ‘yan agaji 20 a hanyar su na dawowa daga aikin jinkai a Zamfara.

An sace wadannan ‘yan agaji ne ranar 23 ga watan Disamba.

Sani Jingir da ya sanar da haka ga manema Labarai a garin Jos ya bayyana cewa an saki wadannan ‘yan agaji ne ba tare da an biya kudin diyya ba.

” An sako su a garin Dauran dake karamar hukumar Zurmi, jihar Zamfara sannan ba a biya ko sisi ba. Wadannan ‘Yan agaji na cikin koshin lafiya.

Jingir ya godewa wadanda suka yi ta yin fadi tashi wajen ganin an ceto wadannan ‘yan agaji

Leave A Reply

Your email address will not be published.