MACE ZA TA IYA BAWA MIJINTA ZAKKA

251

*Tambaya*

Assalamu alaikum. Malam Menene sahihi akan mace tabawa mijnta zakkah ?

*Amsa*
Wa alaikum assalam,

ya halatta a zancen mafi yawan malamai saboda hadisin Zainab matar Abdullahi Dan Mas’ud wanda Bukhari ya rawaito a sahihinsa a lamba ta:(1462) da kuma Muslim a hadisi mai lamba ta: (1000) lokacin da ta nemi fatwa akan bawa mijinta sadaka kuma Annabi S A W. ya halatta mata hakan.
Malaman sun kafa hujja da wannan hadisin saboda kalmar sadaka ta kunshi farilla da sunna .
Aya ta (60) a suratu Attaubah ta yi bayanin nau’o’i takwas na mutanen da ake bawa zakka, daga ciki akwai talaka, hakan sai ya nuna mutukar miji talaka ne matarsa za ta iya ba shi zakka, tun da ba’a samu dalilin da ya fitar da shi ba.

Saidai Ibnul Munzir ya hakaito ijma’i cewa: “Bai halatta miji ya bawa matarsa zakka ba idan tana fama da talauci, tun da zai iya wadatata ta hanyar ciyarwar da Allah ya wajabta masa.

Don neman karin bayani duba: Sharhul Mumti’i (6/168) da kuma Fataawa Allajnah Adda’imah (10/62)

Allah ne mafi sani.

*Dr, Jamilu Zarewa*

21/11 /2017

Comments are closed.