Leken sirrin wayar maigida: Mace za ta yi zaman gidan kaso na wata 3

250

Leken sirrin wayar maigida: Mace za ta yi zaman gidan kaso na wata 3

Wata mace za ta yi zaman gidan kaso har na tsawon watanni uku bayan da wata kotu a Hadaddiyar Daular Larabara UAE ta sameta da laifin sadadawa ta bude wayar mijinta a yayin da ya ke barci, tare kuma da nadar wasu bayanai da suka hada da hotuna da kuma hira da ya yi da wasu a kafar yanar gizo.

Mijin matar ne dai ya maka mai dakin tasa a kotu, inda ya zarge ta da laifin kutsa kai cikin wayarsa ta hannu da nufin bankada sirrinsa.

Kotun da ke zamanta a yankin Ras Al Khaimah da ke a arewacin kasar Hadaddiyar Daular Larabawar ta samu matar da laifin da a ke zarginta da shi.

Mijin nata a yayin da ya ke bayyana kokensa ga kotu ya ce, matar tasa ta nadi bayanai daga wayarsa ta kuma tura wata wayar da nufin ta yi masa kwakkwafi. Sannan kuma ta shiga duk wani lungu da sako na wayarsa ta caje tsaf a lokacin yana barci cikin dare.

Matar ta tura hotuna da hirarraki da mijinta ya yi da wasu ‘yan mata da nufin ta nuna wa ‘yan uwanta.

Sai dai matar ta bayyanawa kotu cewa mijin nata ya bata lambar sirrin bude wayarsa tare da bata damar duba wayarsa a duk lokacin da ta bukatar hakan tun bayan da ta kama shi yana hira da wasu ‘yan mata ta hanyar kafafen yada zumunta na yanar gizo.

Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa na da doka mai tsanani akan laifukan da suka shafi kutsa kai cikin sirrin wani ba tare da yardarsa ba musamman ma ta hanyar amfani da kafar yanar gizo.

Comments are closed.