Kyawawan Hotunan Jarumar Nollywood, Adesua Etomi Sanye Da Hijabi

213

Wasu hotuna da ke ta zagaye a shafukan sada zumunta na nuna shaharariyar jarumar Nollywood din nan mai suna Adesua Etomi sanye da Hijabi.

Dalilin da ya sa wadannan hotuna ke ta zagaye shine yadda suka dasa mutane sakamakon matukar kyan da jarumar ta yi sanye da Hijabin, ta yadda ga wanda bai sani ba ma, zai iya rantsewa Bafulatana ce.

Etomi wacce mata ce a gurin mawaki Banky W ta dauki hotunan ne dai a gurin daukan wani fim mai suna ‘Up North’, inda ta fito a matsayin Zainab.

Za a fara nuna fim din a sinimomi a ranar 28 ga wata mai zuwa Disemba.

Comments are closed.