Kwankwaso ya karbi sabbin mabiya daga masana’antar Kannywood (Hotuna)

200


Siyasa riga yanci kamar yadda malam bahaushe yake fadi, don haka harkace ta ra’ayi, kana ra’yin wani, wani kuma ra’ayi wani daban, masana kimiyyar siyasa sun bayyana wannan banbancin ra’ayin a matsayin abin so a siyasa matukar an tsaftaceta. Legit.com ta ruwaito a yayin da wasu gungun jarumai daga masana’antar Kannywood suka bayyana goyon bayansu ga shugaban kasa Muhammadu Buhari musamman a yayin da ake tinkarar zaben 2019, wasu daga cikinsu sun bayyana mubaya’arsu ga tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso.
A daren Litinin, 10 ga watan Disamba ne wasu fitattu kuma shararrun jaruman finan finan Kannywood suka take ma sakataren hadaddiyar kungiyar yan fim, MOPPAN, Salisu Muhammad zuwa gidan Kwankwaso a Kano inda ya karbi shahadar Kwankwasiyya. Daga cikin jaruman da suka take ma sakatare Salisu baya zuwa gaban Kwankwaso akwai Abba El-Mustapha, Aminu Sheriff Momoh, da shahararren mawakin nan Mudassir Kasim.

Sai dai wannan ziyara da yan fim suka kai ma Kwankwaso yazo ne a daidai lokacin da wani babban jigo kuma jagora a tafiyar Kwankwasiyya, sa’annan na hannun daman Sanata Kwankwaso, Janar Idris Dambazau ya fice daga Kwankwasiyya ya rungumi Gandujiyya. Gwamnan jahar Kano Abdullahi Ganduje ne da kansa ya karbi Dambazau a wani babban gangamin siyasa da jam’iyyar APC ta gudanar da birnin Kano inda gwamnan ya raba tutoci ga yan takarkarun APC da suka samu nasara a zaben fidda gwani. Daga cikin wadanda suka halarci gangamin akwai mai gayya mai aiki Abdullahi Abbas shugaban jam’iyyar APC, dan takarar Sanata a Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, Sanata Kabiru Gaya da Sanata Barau jibrin.

Comments are closed.