Kun san irin talaucin da Mithun da Shah Rukh Khan suka yi fama dashi?

265

Shah Rukh Khan

Jarumin da ake yayinsa wanda aka yi wa lakabi da “Badshah na Bollywood”.

To amma kafin ya kai matsayin da ya kai a yanzu, shi ba wani bane.

Bayan ya yi karatunsa, sai ya je ya fara aiki a wani wurin cin abinci, daga baya ya bude na sa wajen cin abincin, amma daga bisani jarinsa ya karye.

Sai ya koma wani wajen siyar da abincin ya ke aiki cikin masu raba abincin a Delhi.

Albashinsa a lokacin, bai taka kara ya karya ba, amma duk da haka a kullum cikin burin ganin ya zama wani ya ke.

Haka ya yi tayin gwagwarmaya, har Allah ya kai shi matsayinsa na yanzu, inda a cikin jaruman fina-finan Indiyan ma yana daga gaba-gaba a jerin masu kudi.

Ya samu karbuwa sosai a wajen jama’a.

Amitabh Bachchan

Amitabh Bachchan, na daya daga cikin jaruman Indiyan da suka yi fice ba kasarsu ba kadai, har ma a sauran kasashen duniya.

Da farkon dai a rayuwarsa ya so ya zamo mai aiki a gidan rediyo, irn masu gabatar da shirye-shiryen nan, to amma a lokacin da ya je wani gidan rediyo domin aiki sai aka ki daukarsa saboda babbar muryar da ya ke da ita.

Amitabh Bachchan, saboda tsabar neman abinyi a lokacin, yakasance har kwana ya ke a benci a wajen da ya kanje neman aiki.

Haka ya yi ta gwagwarmaya, har da karshe ya samu da kyar aka gwada shi yin fim.

Da farko aidan aka gwada shi, sai aga ba zai iya ba, a haka dai har ya samu aka saka shi a cikin fim.

A yau, Amitabh, na daga cikin masu kudin Indiya ma, ba wai a bangaren jarumai ba kawai.

Mithun Chakraborty

Mithun Chakraborty wanda jama’a da dama suka fi saninsa da sarkin rawa, shi ma ya yi gwagwarmaya a rayuwarsa kafin ya zama wani.

Mithun yakasance a wasu lokuta har kwana ya ke da yunwa saboda tsananin ba bu.

Da farko rayuwarsa ba yabo ba fallasa, amma bayan rasuwar wani wansa kwalli daya tal, sai rayuwarsa ta sauya.

Ya sha matukar wuya wajen fadi tashin neman abin yi, amma daga bisani hakarsa ta cimma ruwa da ya ke yana da wasu abubuwa da za su sa a sanya shi a fim, ciki kuwa har da rawa.

Yanzu yana daga cikin jaruman Indiyan da suka yi fice sosai, kuma ya tara abin hannunsa.

Akshay Kumar

Akshay Kumar, shima fitaccen jarumi ne a fina-finan Indiya, wanda a yanzu haka ma yana daga cikin jarumai maza da suke cajar kudi mai yawa a fim.

Kafin ya fara fim, ya fara aiki ne a matsayin mai dafa abinci a otel d akuma raba abincin ga bakin da suka je otel din a Bangkok.

Ya kan kuma sayar da kayan d aya ke sayowa daga Bangkok idan ya je Indiya hutu.

Daga nan kuma sai ya koma taimakawa wani abokinsa sayar da gidaje da fulotai, anan ne ma ya dan samu abin kansa.

Amma a yau, sai dai ya bayar da gida, saboda daukakar da Allah ya yi masa, da kuma makudan kudin da ya ke da su ta hanyar sana’ar fim.

Dilip Kumar

Tsoho mai ran karfe ke nan, wanda ya bar babban tarihi a fina-finan Indiya.

Dilip Kumar ya fuskanci kalubale kala-kala a rayuwarsa da farko.

Jarumin kafin ya fara fim har duniya ta san shi, ya yi gwagwarmayar neman kudi, domin kuwa har sana’ar sayar da kayan marmari ya yi.

Da ya dan tara ‘yan kudadensa, sai ya je ya bude wani dan karamin shagon sayar da kayayyaki.

A haka- a haka, hat ya samu wani abokinsa wanda babban dan siyasa ne a wancan lokaci ya taimaka shi da kudi ya je domin ya shiga fim.

Ya yi sa’a kuma aka zabe shi. daga nan ne kuma al’amura suka fara canzawa.

Duk da ya ke yanzu ya tsufa sosai har ya daina fim, masana’antar fina-finai ta Bollywood ba za ta taba mantawa da irin gudunmuwar da bayar ba a lokacin da ya ke fim.

Ba a samu jarumin da har yanzu ya kama kafarsa wajen farin jini da iya fim da kuma samun lambobin yabo ba.

Comments are closed.