Karanta Rafkanuwar Neman Aure Guda 12

220


Ka kasancewa lalle ne hakika shi aure ba mataki bane wanda za a dauka sannan kuma a ijiye. Amma sau da yawa mutane suna yin shi ne a rashin sani kuma wannan shi yake haifar da ko dai a samu ingantaccen aure ko kuma a samu aka sin haka.
Wadannan dalilai su ne suka fi tsanani daga cikin, ga su kamar haka;
1. Kana ko kina tsoron rasa masoyi. in dai don jin tsoro ya saka ka yi ko kika yi aure to hakan ba dai-dai ba ne. In dai baka amince da dangantakan ku ba kuma ka yi aure to kawai kamar ka yi cica da kudin ka ne.
2. Matsin lambar abokai ko kuma na iyaye; za ka iya samun matsin lamba daga wasu iyaye ko kuma wasu daga cikin abokai a kan mutum ya yi aure saboda suna tunanin ai lokaci ne. Yana da kyau ka sani cewa wadannan mutanan ba sa cikin auren ka, lalle ne kuma ka sani suna daga cikin wadanda su ke rusa maka aure. Suna daukar wannan mataki ne domin suna tunanin ai lokaci ya yi.
3. Domin ka tsufa; haka ne, amma duk da haka ai lokaci baya kurewa wajen zamantakewar aure. Amma ka sani cewa in dai ba ka yi sa’ar aure ba to sai ka fi kowa nadamar cewa ina ma a ce ka jira kasa mu mutumin kwarai wajen zamantakewar aure ba kamar yadda ake cewa ai lokaci yana tafiya ba.
4. Domin kana ko kina bin bashi; ka ci bashi imma a makaranta ne ko a wajen fati ne ko kuma ta hanyar yin magudi ne? yin aure domin ana binka daya daga cikin abokin zama bashi to wannan ba dubara bane mai kyau. Ka auri wacce kake ma cikakken son, za ka fi gamsuwa da zabin da ka yi.
5. Saboda Kudi; Wannan an fi dangata shi ga mata domin sune suka fi dobin kudi wajen aure. Amma a yanzu maza sun fi so su auri diyan masu kudi saboda suna tunanin duk wata matsala idan ta taso to iyayanta za su warware matsalar. Wannan auren baya yin karko saboda daya zai dunga wa daya gori ko kuma ya raina shi.
6. Saboda Gundura; Ka da ka yi aure saboda baka da wani abin yi a cikin rayuwarka. Kana da tabbacin cewa aure zai kawo makan duk abin da kake bukata. Kai dai ka mayar da hankali wajen abin da zai karawa daga darajarka kamar su wajen fara kauwanci ko kuma duk wata sana’a wacce za ta daga darajarka, idan lokaci ya yi sai ka nemi abokiyar zama.
7. komawa wajen tsohun abokin zamantakewa; baka san cewa tsohun abokin zamanka ya yi aure ba? Za ka iya yin amai sannan kuma ka zo ka lashe? Lalle yin hakan ba dai-dai bane. Lokacin da ka dawo wajen abokin zaman ka to lalla ka sani za ka iya zuwa a same shi da wasu dabi’un da baka so kuma sai ka yi ladamar dawo wanka wajen shi.
8. Ciki; saboda kina da ciki ko kuma ka yi mata ciki shi za ku yi wannan ba ya zama dalilin sai kun yi aure har abada. Wannan zai iya kawo nakasu cikin aurenku saboda za ku dunga tunanin cewa domin dalilin tushanr zamantakewarku shi ne wannan cikin.
9. Saboda kundade tare ; Domin kun dade da juna kuke tunanin shi ne mafita da ku yi aure tare. Wani lokaci bas hi bane, amma duk lakacin da kuka yanke shawarar za ku yi aure, ku tsaya ku yi tunani wai shin ya ya dangantakanku za ta kasance idan kuka haifi yara. Ku kasance masu gaskiya ga kanku da kuma wajen abokanan zaman ku. Haka kawai za ku fara shirye-shiryen aure saboda kuna tunanin shi ne mataki na gaba.
10. Saboda abokaina suna yi; Wannan baya taimaka wa mata wajen kwatanta kansu da kuma sa’o’insu domin ci gaba. Muna yawan samun damuwa wajen ganin lalle sai mun yi aure saboda dukkan abokanmu sun yi. Amma shi aure abune wanda gaba dayansa abune na radin kanka. Bai kamata a ce don wacan ya yi ba kaima ka ce sai ka yi. Ya kamata ka tsaya ka tabbatar da cewa kai da kanka ka na jin cewa lalle ka shirya kafin ka yi.
11. Domin iyayaenka su kadai ne; Bai kama ka yi aure ba saboda ganin cewa ‘yan’uwanka ko kuma iyayenka su kadai ne, wannan ba dalili bane wajen nuna masu soyayya da kuma kauna na har abada. Ka tabbatar da cewa za ka yi auke ne saboda ka shirya da kuma soyayya mai karfi a tsakain ku.
12. Kana tunanin cewa shi mataki na gaba; domin ka gama karatu ko kuma ka samu karin girma a wajen aiki. Domin ka saya babban gida ko kuma ana tunanin cewa kakai wani shekaru. Ko wani irin dalili kake da shi dai, bai kamata ka yi aure ba domin kana tunanin shi ne mataki na gaba. Ba a yin aure a matsayin kamar tsarin sunayen abin da za ka ai water a cikin rayuwarka. Mafi yawan mutane sun yin aure ne ba tare da sun shirya ba ko sun yi tunani ko kuma su yi auren domin wani abin da suka mallaka, saboda haka aurensu ya auka cikin matsala sakamakon rashin kyakkyawan tsarin aure.

Leave A Reply

Your email address will not be published.