Karanta KuJi Yanda Dan Shekara 70 Ya Aure Yar Shekara 15

364

Wani tsoho a jahar Niger mai suna Yakubu Chanji ya auri wata matashiya ‘yar shekaru 15 a duniya.

Makotan mutumin sun fadawa jaridar Daily Nigerian cewa Chanji ya haura shekaru 70 a duniya.

Rahotanni sun bayyana cewa an daura auren ne a jiya Litinin a karamar hukumar Lapai da ke jahar.

Chanji wanda aka kuma ake kira Nafsi Nafsi a garin Minna ya samu wannan inkiya ne a sakamakon halinshi na auri saki da chanja mata kamar tufafin sakawa, kamar yadda makota suka shaidawa jaridar.

“A iya sani na, ya sauya mata ya kai sau 12. Amma wasu na ganin ya kai sau 20.” Inji wata majiya.

“Abunda muka sani shine, a koda yaushe ya na zaune ne da mata hudu. Da zaran ya saki daya ko daya ta mutu, sai ya sake auro wata” Inji wata majiyar daban.

Wata majiya ta bayyana cewa ya na taimakawa Al’ummar yankin Kwangila da ke Minna da dukiyarshi musamman a yayin gina masallacin yankin.

Comments are closed.