Karanta Kadan Daga cikin Amfanin Albasa Ajikin Dan Adam

251

Daga cikin Fa’idodin da
ALBASA take Qunshe
dashi, zamu gutsuro
muku wasu ‘yan kadan
kamar haka:
1. Albasa tana tacewa
jinin jikin ‘Dan Adam.
Duk mutumin da yake
fama da matsalar
Qarancin jini, ya yawaita
cin albasa. insha Allahu
jininsa zai yawaita.
Wanda yake fama da
ciwon SICKLE CELL
ANEMIA, ya rika yanka
albasa tare da Ganyen
Zogale yana ci. Insha
Allahu wannan ciwon
Sickler din zai yi sauki.
2. MAGANIN TARI :
Wanda yake fama da tari
ko mura mai tsanani, ya
nemi Man Albasa kamar
cokali 9, zuma cokali 9.
A gauraya arika shan
cokali uku bayan
kowanne cin abinci.
Insha Allahu Ciwon Qirjin
zai warke, Kuma tarin ma
za’a dena.
3. RASHIN YIN BAWALI :
Wanda yake shan wahala
wajen yin fitsari ko
bahaya, Ka nemi Man
albasa ka gauraya da
zuma da lemon tsami. ka
rika sha safe da yamma.
kuma ka rika shafa man
albasa ajikin Mararka.
Insha Allahu zaka samu
waraka cikin lokaci
kankani.
4. CIWON SUGAR : Duk
mai fama da yawan fitar
fitsari saboda diabetes
(Ciwon Sugar) ya nemi
albasa mai kyau ya rika
yankawa kullum yana ci.
Insha Allah sugansa zai
sauka, kuma zai dena
yawan fita fitsarin.
5. ZUBEWAR GASHI : duk
matar da take fama da
zubewar gashi, ko
kwarkwata, ko amosani,
ta samu Ruwan albasa,
Man Simsim, da kuma
garin Baqadunas. ta rika
shafawa a matsirar
gashinta kullum kafin ta
kwanta barci. idan ta
farka sai ta wanke da
ruwan zafi. ta ci gaba da
yin haka har tsawon
kwana bakwai.
Insha Allah zata samu
waraka sosai.

Comments are closed.