Karanta Jerin Sabon Albashin Yan Sandal Najeriya

211

Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan takardan Karin albashin ma’aikatan hukumar yan sandan Najeriya a ranan Litinin, 26 ga watan Nuwamba, 2018.
A farkon watan nan, Wasika daga hukumar albashi ya nuna cewa an karawa jami’an yan sandan Najeriya albashi. Shugaba hukumar Cif Richard Onwuka Egbule, ya rattaba hannu kan wannan wasika bayan samun umurni daga ofishin hukumar.
Wasikar tace: “Ina mai tabbatar da Karin albashi da canjin tsarin albashin hukumar yan sanda. Wannan kari zai fara aiki ne daga ranan 1 ga watan Nuwamba, 2018 kamar yadda fadar shugaban kasa ta tabbatar.”

1) Konstable (PC) II – N84,000
2) Konstable (PC) I – N86,000
3) Sajen Kofura (SC) – N96,000
4) Sajen Major (SM) – N119,000
5) Sifeto (IP) II – N167,000
6) Sifeto (IP) I – N254,000
7) (ASP) II – N271,000
8) (ASP) I – N296,000
9) Mataimakin sufritandan (DSP) – N321,000
10) Sufridtandan (SP) – N342,000
11) Babban Sufritandan (CSP) – N419,000
12) Karamin mataimakin kwamishana (ACP) – N483,000
13) Mataimakin kwamishana (DCP) – N531,000
14) Kwamishana (CP) – N1.5million

Comments are closed.