karanta ILLolin Nisantar Jima’i Ga Ma’aurata

6,751

Ma aurata ga junansu ko kuma inche qaurachewarsu ga juna, ko kuma haka kawai namiji ya dau alwashin daina mu’amalar aure da matarsa, ko kuma ita matar ta dau wannan matakin. A matakin kiwon lafiya da kuma masanan alaqar dake tsakanin halittar namiji da mache.

Ana kiran wannan abu da
ﺍﻟﺠﻮﻉ ﺍﻟﺠﻨﺴﻲ
Ma’ana: YUNWAR JIMA’I:

Binchike kuwa ya tabbatar da hadarin yunwar jima’i. Wanda da wahala mai irin wannan yunwar ka same shi mai natsuwa ko kwanchiyar hankali. Wasuma takan kai su ga samun matsala a hankalinsu ko kuma su zama dolaye ko su dinga shirme a ayukkansu na yau da gobe gangar jikinka shi ke da buqatar abinchi.

Ruhinka kuma shi ke da buqatar jima’i
da yawan masu binchike suna ganin yunwar saduwa tafi illa tare da lalata jikin dan adam fiye da yunwar abinchi.

Sun bada misalai da dama akan mata masu shekaru iri daya wannan ta yi aure kuma aka yi dache ta sami kwanchiyar hankali achikin aurenta. Ita kuma dayar ba ta yi aure ba.

To zaka fahimchi damuwa da rashin sukuni ga wacche bata yi auren ba, saboda tana fama da matsalar yunwar saduwa. Sun che yunwar saduwa tafi qarfin ayi mata dabara kuma ta gagari duk wani numfashi.

Masana da Malamai sunche duk wanda zaka ji yana qaryata sha’awa to kodai maqaryachi ko kuma bai da lafiya. An sami manyan Malamai da sha’awa ta chi qarfinsu an kuma samu masu Sarauta duk tarihi ya tabbatar. Hasalima ya zo a hadisi Manzon Allah (S. A. W) ya che:

ﻻﺭﻫﺒﺎﻧﻴﺔ ﻓﻲ ﺍﻹﺳﻼﻡ

Ma’ana:
musulunchi bai yadda kaita ibada ba kokuma kaqi aure saboda ibada.
Tabbas akwai matsaloli da zasu iya samun jikin ma’auratan da suka qaurachewa juna.
Ga kadan daga chikin matsalolin:

* ﺍﻟﺸﻌﻮﺭ ﺍﻟﺰﺍﺋﺪ ﺑﺎﻟﺘﻮﺗﺮ

Ma’ana matsananciyar damuwa ga matar da mijin.

Domin mu’amalar auratayya tana taimakawa wajen fitar da dogon numfashin da ke tafiyar da damuwa da bakin ciki ya samar da hutu da natsuwa.

*Abu na biyu shi ne:

ﺗﺰﺍﻳﺪﺧﻄﺮ ﺍﻹﺻﺎﺑﺔ ﺑﺴﺮﻃﺎﻥ ﺍﻟﺒﺮﻭﺳﺘﺎﺗﺎ
Wannan bincike na biyu wata jami’a ce a America suka gano cewa tabbas ma’auratan da basa kusantar junansu to sai sun fi kamuwa da cancer ta al’aura
Mijin da kuma matar zasu iya kamuwa da cututtukan al’aura dukkansu.

Abu na uku:
ﺍﻹﺻﺎﺑﺔ ﺑﺎﻟﺒﺮﺩ

Ma’ana kamuwa da cutar sanyi
Ko a yanzu kuwa zamu ga ‘yan matan mu sun fi matan aure zama da wannan cuta ta sanyi.
Abu na gaba shi ne:

ﻓﻘﺪﺍﻥ ﺍﻟﻘﺪﺭﺓ ﺍﻹﻧﺘﺼﺎﺏ

Ma’ana duk namijin da zai dade bai kusanci iyalinsa ba to zai zama marar kuzari.

Akwai abin dana gani akan matsalolin al’aura na maza tabbas wannan matsalar tana shafar hadda maza masu mugun dadewa basu yi aure ba.

Abu na gaba shine
ﺍﻟﺸﻌﻮﺭ ﺑﺎﺍﻹﻛﺘﺌﺎﺏ
Ma’ana yawan gajiya ko kasala
Wannan kuma wata mujallache mai suna
(Archives of Sexual Behaviour)
Sun tabbatar da babu abin da ke qarfafa gabobi kamar kusantar juna akan qa’ida.

Takaiche dai ko a musulunchi ba’a so miji ya haura watannin iddar mutuwa bai kusanchi iyalinsa ba.

LOKUTAN DA KUSANTAR JUNA YAKE IYA ZAMA MATSALA:

・ A duk lokachin da ango ya tabbatar ya kawar da budurchin amaryarsa to haqiqa ya qaurache sake kusantarta sai aqalla bayan kwana uku ko hudu in kuwa ya kasa haquri to akwai yi yuwar shida ita suhadu da chutar al’aura ita ake kira da (Infection) shi kuma sai abinda ya gani.

・ Dole a haqura da juna a lokachin haila da lokachin jego yin jima’i a lokachin yana iya haifar da chutar (Cancer).

・ A haqura da saduwa a lokachin da ake da muguwar gajiya da kuma matsananchiyar damuwa.

・ A nisanchi saduwa lokachin da ki ke fama da matsalar (Infection) domin indai zaki yi jima’i ba zaki warke ba.

・ A guji saduwa a lokachin da Oga ke fama da quraje a gabansa har sai ya warke.

・ A kuma guji saduwa a lokachin da daya daga chikin ma’aurata ya kamu da daya daga matsalolin da ake samu a wajen saduwa.

Wannan a taqaiche kenan Allah yasa za’a amfana da wannan ‘yar fadakarwa
Allah kuma ya taimake mu ya yi mana jagora a chikin dukkan al’amuranmu ya sadamu da farin chiki a duk wata mu’amala da zamuyi
Dan’uwanku a Musulunchi…

1 Comment
  1. HARUNA says

    Wannan kafa taku tana amfanar damu sosai mungode.

Comments are closed.