Kannywood :- Sunayen jaruman da keda sarauta a masarautu daban daban

102


Jaruman Kannywood 5 dake da mukamin sarauta a masarauta daban daban kwanan nan Mun hada jerin sunayen jarumai 5 da suka samu damar karban sarauta daga masarauta daban daban kwanan nan.
Ga jerin jaruman kamar haka:
1. Muhammed Ibrahim Mandawari (Mai Unguwar Mandawari) Wannan fitaccen tsohon jarumin kannywood ya gaji mahaifin sa inda Sarkin Kano Mai Martaba Muhammad Sanusi na biyu ya nada shi a matsayin “Mai unguwar” yankin Mandawari nan garin kano.
2. Sani Danja (Zaki Yan wasan Arewa) Dan zaki kamar yadda ak fi kiran shi yayi bikin nadin sarautar “Zaki yan wasan Arewa” yayin da sarkin nupawa a nada a jihar Niger. Etsu Nupe ya nada shi da sarautar ranar 25 ga watan agusta a nan garin Bidda dake jihar Niger.
3. Maryam Gidado (Innawuron Zamfara) Kungiyar masu shirya fina-finai ta arewa na Arewa film makers association ta nada ta a matsayin “Innawuron Zamfara” ranar 4 ga watan nuwamba a Gusau babban birnin jihar Zamfara.
4. Rasheeda Abdullahi Mai sa’a (wakiliyar Arewa) Ita ma Jaruma Rasheeda mai sa’a ta samu sarautar “Wakiliyar arewa” daga kungiyar AFMAN a garin Minna babban birnin jihar Niger cikin watan Octoba na bana.
5. Fati Niger (Gimbiyar Arewa) Mawakiya Binta Labaran wanda aka fi sani da fati Nijar ta samu sarauatar “Gimbiyar arewa” rana daya da Rasheeda.

Leave A Reply

Your email address will not be published.