Kannywood: Rahama Sadau ta bayyana alakar da ke tsakaninta da Akon

238


Fitaciyar jarumar Kannywood Rahama Sadau tayi tsokaci kan ikirarin soyayar da aka ce tana yi da mawakin Amurka, Aliane Damala Bouga wanda akafi sani da Akon.

A hirar da akayi da ita a shirin Kundin Kannywood da ake nunawa a tashar Arewa 24 TV a ranar Talata da Aminu Sharif Momoh ke gabatarwa. “Ban taba tsamanin zan hadu da Akon ido da ido ba. Na san wakokinsa tsawon shekaru masu tsawo saboda shi mawaki ne da ya yi suna sosai. Saboda haka nayi matukar murna lokacin da ya gayyaci ni kuma na amsa gayyatar,” inji Sadau.
kan zargin da akeyi na cewa mawakin ya nemi ta canja addini zuwa Kiristanci, Sadau ta ce hakan ba gaskiya bane domin duk wanda suka san shi ba za su fadi hakan ba domin shi musulmi ne kuma yana da matan aure uku. “Wasu sun fada min cewa lokacin watan Ramadan, ya kan kebe kansa daga mutane saboda ya samu ikon gudanar da ibada,” inji Sadau.
Rahama Sadau ya bayyana cewar Akon ya gayyaci ta zuwa Umara tare da iyalansa amma ba ta amince ba saboda kaucewa zargin da wasu mutane za su rika yi game da hakan. Har ila yau, Jarumar ta yiwa mutane albashir da sabon fim din ta mai suna “Mati Zazzau” wanda zai fito nan ba da dadewa ba.

Comments are closed.