Kannywood -Abida Muhammad: Bana sha’awar komawa fim

109

Fitacciyar tsohuwar jarumar fina-finan Hausa ta masana’antar Kannywood Abida Muhammad ta bayyana cewa ko kadan bata sha’awar dawowa harkar shirya fina-finan Hausa kwata-kwata. Ta qara da cewa tun da ta bar harkar ta tafi gidan mijin ta sai sana’ar ta bar bata sha’awa kwata-kwata. Abida Muhammad wadda ta haskaka sosai a lokutan baya musamman a cikin fina-finai da dama tayi aure da dadewa inda ta zauna a dakin mijin nata har Allah yayi masa rasuwa.

Masana harkokin fina-finai da dama dai na da ra’ayin cewa tsohuwar jarumar na daya daga cikin jaruman da Allah ya azurta da dimbin basira da ta bar gibin da kuma har yanzu ba’a cike ba a masana’antar.
Fimhausa

Leave A Reply

Your email address will not be published.