KAKATA BA TA IYA SALLAH SABODA RUDEWA KO ZA TA FADI AKANTA?

229

KAKATA BA TA IYA SALLAH SABODA RUDEWA KO ZA TA FADI AKANTA?

*Tambaya*

Assalamu alaikum ina fatan Dr yana cikin koshin lafiya, Allah ya kara masa imani da fasaha Amin.Dr kakata ce tsufa ya kamata ga rashin lafiya, yaranta tara bata gane Ko daya daga cikin su gashi bata gane alwala balantana Sallah, Ko an mata alwala bazata gane Sallah ba, ga shi tana yini da pampas a jikinta ya zamuyi da sallanta???

*Amsa*

Wa alaikum assalam Ku yi iya ba-kin kokarinku wajan Ku ga ta kwatanta sallah, in bai yiwu ba ku kyale ta, saboda Allah ba ya dorawa rai abin da ba zai iya ba kamar yadda aya ta karshe a Suratul Bakara ta yi bayanin gamsashshe akan hakan.
A zahirin nassoshin sharia in har ba ta gane komai to za ta dau hukuncin Mahaukata ne, tun da ba ta cikin hayyacinta,
mahaukaci hadisi ya tabbatar da sarayuwar sallah daga kansa.

Sallah ba ta karbar wakilci, don haka ba Wanda zai rama mata a cikinku.

Allah ne mafi sani

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

11/11/2018

Comments are closed.