INA SON BAYANI AKAN ‘YAN TABLIG, SABODA MIJINA YANA BIN SU?

247

*_INA SON BAYANI AKAN ‘YAN TABLIG, SABODA MIJINA YANA BIN SU?_*

*Tambaya*
Assalamu alaikum . Da fatan Malam yana lafiya . Dan Allah ina son bayani akan tabligh da mutanen pakistan suka assasa kuma suke yawon da’awa suna kiran mutane su fita da’awa na wasu kwanaki ko watanni, Mijina ya shiga kuma zai tafi kwana 40 amma ni hankali na ya ki kwanciya da hakan . Jazakallah .

*Amsa:*
To ‘yar’uwa ‘yan tablig wasu jama’a ne wadanda suka sanya da’awa i zuwa ga Allah babban aikinsu, kuma mutane ne masu gudun duniya, in sun je gari da’awa ba sa sauka wajan kowa, saidai şu shiga masallaci, suna dagewa sosai wajan da’awa duk alhamis a wasu kasashen, Muhammed Yûsuf Al-kandahlawy Ba’indiye wanda ya mutu a shekara ta:1364 bayan hijira shi ne ya kafata.

Saidai akwai kura-kurai da yawa a tafiyarsu, daga cikin akwai:
1.Karancin ilimi, ba şu damu şu yi ilimi mai zurfi ba, ko dan yaya şu ka Samu sai şu tsunduma çıkın da’awa.
2. Ba şu damu da hana aikata mummuna ba, şuna karfafa da’awarsu ne wajan umarni da ayyukan da Allah ya ke so.
3. Suna da karancin ilimin tauhidi, sun fi damuwa da bayanin falalolin ayyuka.
4. Suna kafa hujja da hadithai raunana da na karya.
5. Wasu daga cikinsu suna sakaci da hakkokin iyalansu, saboda shagalarsu da da’awa.
6. Sukan aibanta malaman da ba sa cikinsu, da rashin damuwa da Şakacı da da’awa.
7. Karancin iliminsu yana jawo musu fadawa kura-kurai wajan fassara Al’qur’ani.

In har kin san mijinki yana da karancin ilimi zai fi kyau ki sanya a tsawatar masa, game da bin su don kar ya fito kafin ya nuna, duk wanda ya zamar da kansa malami kafin ya isa, barnarsa za ta fi gyaransa yawa.

Allah ne mafi sani

13/03/2016

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Comments are closed.