INA CIKIN IDDA, SAI WANI YA YI ZINA DA NI ! YAYA ZAN YI ?

1,638

INA CIKIN IDDA, SAI WANI YA YI ZINA DA NI ! YAYA ZAN YI ?

Tambaya :
Malam mijina ya sake ni, bayan na yi tsarki daya, sai rikici ya kaure tsakanin arna da musulmai a garinmu, sai wani crister, ya dauke ni ya yi zina da ni, yanzu malam yaya zan yi game da idda ta ?

Amsa :
To ‘yar’uwa ina rokon Allah ya kawowa musulmi dauki a Nigeria, wannan mas’alar ta ki malamai sun yi sabani akanta, akwai malaman da suka tafi akan dole sai kin yi istibra’i bayan kin gama idda, saidai maganar da tafi zama daidai ita ce : kawai za ki karasa iddarki ne, ba sai kin yi istibra’i ba bayan kin kammala, saboda babbar manufar istibra’i ita ce kubutar mahaifa, hakan kuma zai tabbata idan kika karasa jinane biyun da suka rage miki na iddarki.
Yana daga cikin saukin addinin musulunci kasancewar duk ibadojin da za su iya shiga cikin juna kuma manufarsu daya ce, jinsinsu guda ne, to daya za ta shiga cikin daya, kamar wacce ta yi jima’i sai kuma haila ta zo mata, wanka guda daya ya ishe ta a karshen hailarta.
Allah ne mafi sani.
Duba : Majmu’ul fawa’id na Sa’ady shafi na : 141.

Jameelu Yusuf Zarewa
25/12/2014

Comments are closed.