Ganduje ya zantar da hukunci kan dakatarwar da aka yi ma jaruma Rahama Sadau

156


Rahotanni sun kawo cewa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya dage dakatarwan da kungiyar kula da da’an masu shirya fina-finan Hausa ta MOPPAN ta yi wa Rahama Sadau.
Kungiyar yan wasan Hausa na jihar Kano ta yaba ma gwamna Ganduje bisa wannan mataki da ya dauka n adage takunkumin da aka sanya ma jarumar.
Shugaban kungiyar Alhaji Alhassan Kwalli bayyana cewa wannan matakin na da amfani matuka a daidai wannan lokaci da masana’antar fina-finai hausa ke kokari wajen samar da cigaba a kasar ta hanyar ayyukan ta.
A cikin takardar wanda mataimakin sakataren kungiyar Rabiu Rikadawa ya fitar a ranar litinin, yayi ma gwamnan godiya kan daga dakatarwar da aka yi ma Rahama Sadau.
Kungiyar ta kuma jinjina ma mai girma gwamna bisa goyon baya da yake baiwa masana’antar fina-finan hausa da ma jaruman cikin ta.
Idan dai ba zaku manta ba kungiyar MOPPAN ta dakatar da jaruma Rahama tun bayan fitowa da tayi a wani bidiyo na mawaki Classiq wanda ya saba ma dokar kungiyar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.