Duk wanda zai aureni sai ya ban motoci 3, shanu 530 da dalar Amurka 10,000–Inji wannan rangadediyar budurwar

220

Wata ‘yar Sudan ta Kudu ta wallafa hotonta a Facebook don neman mijin aure,inda ta ce za ta aure duk wanda ya ba ta shanu 530, mota samfurin V8 guda 3 da dalar Amurka dubu 10,000 a matsayin sadaki.

Matashiya Nyalong Ngong Deng Jalang (A hannun dama a hoton labari) mai shekaru 16 da haifuwa ta yi fice haikan a duniya,sabili da yadda aka dinka yada hotunanta a kusan dukannin shafukan sada zumunta.
A yanzu akwai maza biyar da ke ci gaba da gogayya da juna don auren budurwar.
Tashar rediyon Sudan ta Kudu,Tamazuj ta sanar da cewa,a sahun wadanda ke kai ruwa rana don samun amincewarta har da wani sanannen kusa na gwamnatin kasar.
Tuni matasa daga sassa daban-daban na cikin wajen kasar Sudan ta Kudu ke ci gaba da cincirindo a Facebook don gwada sa’arsu wajen daukar wannan allurar cikin ruwa,inji su.
TRThausa.

Comments are closed.