Dandalin Kannywood: Takaitaccen tarihin fitacciyar jaruma, Fati Washa

263Fatima Abdullahi Washa kamar yadda asalin sunan ta yake ba bakuwa bace a harkar fim din Hausa don kuwa ta fito a fina-finai da dama inda tayi fice Duniya ta san ta

- Jama’a sun fi sanin ta da Washa ko Fati Washa watau sunan Mahaifin ta ya bace.
Jarumar tana lokaci, tana samun aiki fiye da duk wata jaruma domin acikin fim biyar sai ka samu ta fito a uku ko hudu, daga cikin tsoffin finafinanta akwai Sarki.

Kadan daga cikin fina-finan wannan Jaruma akwai Ya Allah daga Allah, da tayi a 2014, 'Yar Tasha a 2015 Washa ta fito a Ana Wata ga Wata a shekarar 2015. Sannan ta fito a Mijin Biza, Hindu, Dangin miji, Matar Wani da sauransu.

Akwai jita-jita da take yawo akan Jarumar tana soyayya da Jarumi Adam A Zango, duk dai basu fito fili sun tabbatar ko karyata hakan ba, Amma kowa ya yadda fati washa tafi kowace jaruma kusa da Adam A Zango domin tun daga fim din Sarki har yanzu suna tare.
Fatima ba ruwanta da fada da kowa domin tunda take ba'a taba jinta da wani ko wata ba suna rigima ko kuma jan fada.

Comments are closed.