Dandalin Kannywood: ‘Auren’ Jaruma Maryam Booth da Sadiq Zazzabi ya bar baya da kura

265


Irin ce-ce-ku-ce da surutan da ake ta faman yi a tsakanin ma’abota kafofin sadarwar zamani musamman ma masu sha’awar kallon fina-finan Hausa kan wasu hotuna da fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood Maryam Booth ta wallafa na bikin aure a iya cewa ya bar baya da kura.
Jarumar dai ta wallafa hotunan ta tare da Sadiq Zazzabi mawakin Hausa a cikin wata shiga irin ta ango da amarya, hotunan da ke nuna kauna da soyayya tsantsa tamkar da gaske.
Hotunan sun ja hankalin mabiyanta da ma’abota fina-finan Hausa sosai inda akayi ta yada hutunan a shafukan sada zumunta na intanet cewa Maryam Booth za ta yi aure. Legit.ng Hausa ta samu cewa yayin da wasu ke tunanin a fim ne, wasu kuwa cewa sukeyi da gaske ne za ta auri Sadiq Zazzabi ganin cewa mawaki ne da ba ya fitowa a fim. Sai dai binciken majiyar mu da ta tuntubi Maryam Booth domin tabbatar da ko da gaske ne za ta auri Sadiq Zazzabi ya tabbatar da cewa shirin fim ne kawai ba da gaske bane.

Comments are closed.