Dandalin Kannywood: Atiku Abubakar ya sa labule da jaruman ‘yan fim din Hausa

255


Jaruma Fati Mohammed da Jarumi Aminu Shareef Momo sun Jagoranci tawagar Yan masana’antar shirya fina finan Hausa Kannywood zuwa wajen dan takarar Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar don nuna cikakken goyon baya.

A lokacin ziyarar Jaruman sun bayyanawa Alhaji Atiku Abubakar cewar zasu yi amfani da shafukan su da masoyan su wajen mara mishi baya domin cimma gaci.
Dandalin Kannywood: Atiku Abubakar ya sa labule da jaruman ‘yan fim din Hausa

Majiyarmu Hausa ta samu cewa a lokacin ziyarar baya ga Fati Mohammed da Aminu Shareef Momo an ga fuskokin Jarumai da dama ciki harda Balarabe Jaji da Zaharaddeen Sani da Nura Zarge da sauran Manyan Jarumai. A wani labarin kuma, Tuni dai jarumai irinsu Adam A. Zango da Fati Shu’uma da makamantansu suka bayyana goyon bayansu ga Shugaba Muhammadu Buhari. Masu sharhi na ganin jaruman Kannywood ka iya sauya akalar zaben 2019, wanda aka kaddamar da yakin neman zabensa ranar Lahadin da ta wuce.

Comments are closed.