Dandalin Kannywood: Ana zargin soyayya mai karfi a tsakanin Adam Zango da Fati Washa

1,607

A dan iskan nan mai kadawa maganganun dake ta yawo a bakunan jama’a dai yanzu shine irin so da kauna mai karfin gaske da a ke zargin ya shiga tsakanin fitattun jaruman nan na wasan Hausa fim a masana’antar Kannywood watau Adam Zango da Fati Washa.
Wannan dai na zuwa ne lokacin da hotunan jaruman biyu a tare cikin raha da daman gaske ke cigaba da bayyana a kafafen sada zumunta na zamani inda kasafai ake ganin su suna ta raha suna dariya.


Legit.ng haka zalika ta samu cewa masu sharhi akan al’amurran yau da kullum a masana’antar shiya fina-finan ta Kannywood sun lura da cewa yanzu fina-finan da jaruman biyu keyi a tare na ta kara yawa a kasuwanni. Sai dai kuma duk da maganganun dake ta yawo a kan lamarin, har yanzu jaruman sun ki fito su tabbatar ko kuma su karyata batun wanda hakan ke kara darsa kokwanto a zukatan masu sha’awar fina-finan.

@NaijHausa

Comments are closed.