Dandalin Kannywood: Allah bai wajabta mani in yi aure ba – Inji Shehiyar malama Ummee Zee-Zee

107

Dandalin Kannywood: Allah bai wajabta mani in yi aure ba – Inji Shehiyar malama Ummee Zee-Zee

Shahararriyar tsohuwar jaruma a wasan fina-finan Hausa mai suna Ummee Zee-Zee ta fito ta fadawa duniya cewa Allah fa bai wajabta aure ba akan dukkan mutane don haka a shafa mata lafiya. Kamar yadda muka samu daga majiyar mu, jarumar ya yi wannan kalamin ne kusan a matsayin raddi ga al’umma mutane da ke ta caccakar ta da kuma ire-iren ta da cewa sun ki suyi aure duk kuwa da cewa shekarun su sun ja.

Read more: Dalilin da ya sa na fito a Barauniya — Hafsa Idris (barauniya)

Majiyarmu dai ta samu cewa a kwanan baya ma dai wata tsohuwar jarumar a masana’antar fina-finan Hausa Fati Muhammad ta fito ta bayyana babbar nadamar ta a rayuwa a matsayin auren dan fim Sani Musa Mai iska da tayi a shekarun baya.

Read more: Kannywood:Yadda Nafisa Abdullahi tayi kaca-kaca da Rahma Sadau

Su dai jaruman fina-finan Hausa musamman ma dai mata a cikin su na fuskantar matukar matsin lamba daga al’ummar Hausa inda kuma a lokuta da dama akan zarge su da bata tarbiyyar jama’a.

Naij

1 Comment
  1. www.Muhammedbnd.com says

    Enter your comment… Hakatake

Leave A Reply

Your email address will not be published.