Dan Shekaru 19 Ya Auri Mata Mai Shekaru 39 a Duniya (Hotuna)

413

A wasu hotuna da ke ta yaduwa a shafukan sada zumunta, an ga wani ango mai shekaru 19 tare amaryarsa mai shekaru 39.

Babu wani cikakken bayani game da wadannan sabbin ma’aurata, illa dai kawai abunda hotunan suka nuna.

Wani ma’abocin amfani da shafin Facebook, Akulo Sam Ochen shi ya fara yada wadannan hotuna, inda ya ce shekaru ba su da muhimmanci idan da soyayya, sannan ya bayyana shekarun ma’auratan.

A hotunan, wannan matashin ango ya sanya jallabiya da ishrami irin na larabawa, inda ita kuma amaryar ta sanya doguwar riga da lullubi irin na amare.

Comments are closed.