Dalilina Na Hana Wata Mace Yin Zikiri – Malam Ibrahim Khalil

154

A wannan makon, Editan LEADERSHIP A YAU LAHADI, NASIR S. GWANGWAZO, ya cigaba da tattaunawa kan da shahararren malamin addinin Islama din nan kuma gagarumin dan siyasa, manomi, dan kasuwa, wato MALAM IBRAHIM KHALIL. Shehin malamin ya cigaba da bayani kan irin yadda wasu mutane ke kasa fahimtar sa bisa irin fatawoyin da ya ke bayarwa. Tafaddal:

Mutane su kan kasa fahimtar yadda na yi wani hukuncin na fatawa; misali akwai lokacin da wata mace ta bugo waya a filin Fahimta Fuska cewa ita ta yi shakara da shekaru ta na rokon Allah (SWT) ya kai ta Makkah, amma ba ta je ba. Ta ce ta yi zikiri, ta yi addu’a har ta kai matsayin da idan ta ga an biya wa wata mace ko wani mutum Makkah, sai ta dinga ganin cewa me ya sa yanzu ita da ta yi shekara da shekaru ta na rokon Allah (SWT) ya kai ta Makkah, amma bai kai ta ba, ga shi a na ta kai wasu. Sai na ce da ita to ta daina zikiri da addu’a don ta je Makkah, ta daina komai ta hakura kawai kuma kada ta sake rokon Allah ya kai ta Makkah. Kawai ta watsar da wannan ta kama rayuwarta. To, sai wani ya same ni ya ce, ‘yanzu Malam ka ce mace ta daina rokon Allah?’ Na ce, ‘eh’.
To, su mutane ba su san me na ke nufi ba, sai na ce ma sa ‘ka ga saboda ta na yin zikirinta da addu’arta ta zo ta na zargin Allah a kan ya ki ya taimake ta har kuma ta zo ta na jin haushin wadanda Allah ya sa a ka biya mu su Makkah. Don haka wannan mummunan tunanin ya na cutar da ita kuma ya na nisanta ta da Allah (SWT)’. To, su ba su san me na ke nufi ba; na ce kawai ta bayar da lambar wayarta a ajiye. Bayan ta manta ma na je na samu mai kamfanin jiragen sama na Azman na ce Ina neman alfarma idan lokacin aikin Hajji ya yi ya bada kujera guda daya ga wata mace. Ya ce idan lokacin ya yi za a ba ta. Don haka da lokacin aikin Hajjin shekarar ya zo na je na tuna ma sa, sai ya ce, to. Ka ga a ka ba ta kujera a ka ce duk komai da komai an dauke ma ta. Abinda kawai da ba za a ba ta ba shi ne guzirin abincin da za ta ci da na motar da za ta hau daga gida zuwa harami da hadaya, wanda daga baya wannan din ma a ka zo a ka taimaka a ka ba ta.
To, mutane ba sa iya fahimtar me ya sa ka ke daukar wani matsayin da kuma ka ceci ran ita wannan mata da ta ke yiwa Allah kallon cewa ba ya taimakon ta. Kamar yadda ta fada ta na ganin ta yi addu’ar nan ba ta kai ta Makkah ba, amma sai ta ga an biya wa wata mace wacce ta na ganin ba ta fi ta rokon Allah ba ko kuma ba ta damu da abin yadda ita ta damu da shi ba. Ta ce shekara guda ta ke yi ta na rokon Allah, amma idan shekara ta zo ba ta je ba, sai ta sake yin wata shekara guda din har ta yi kusan shekara goma, amma Allah ya ki kai ta Makkah. To, yanzu wannan ka ga saboda tunaninta tsakaninta da Ubangijinta ne ya sa na ce ta daina zikirin, don kada ya raunana imaninta ta ga kamar addu’ar da zikirin ba su da amfani. To, sai wani ya ke ganin don me zan ce a daina zikiri da rokon Allah? To, ka ga irin wadannan su ne da mutane ba sa gane meye dalili.
To, amma kamar misalin da ka bayar a makon jiya na macen da ta yi limanci a Amerika, kai kuma ka sadaukar da kanka ka dauki gabaran hatsarin lamarin ta hanyar bada fatawar da ta mara wa matar baya, don gudun kada a samu barkewar tarzoma duk da cewa hakan zai bata wa malamai da mutane da dama, shin ba ka tunanin hakan zai iya sa wa wasu malaman su tunzuro jama’a har su iya kai ma ka farmaki?
Ai ba za a zo a kawo min hari ba. Abinda kawai za a min shi ne zagi, cin mutunci da cewa Ina wasa da addini ko ba na ganin girman addini. A nan za ta kare…
To, ba ka ganin cewa, wannan abin damuwa ne?
Me zai sa na damu, bayan na san alheri na yi? Ai zuciyata ba ta taba tayar da hankali, don na yi fatawa an zage ni ba. To, Sidi Abdulkadir Jilani ya na cewa duk ranar da ka yi hukunci a ka zage ka a kan abinda ya ke daidai, sai ka gode wa Allah cewa ka shiga layin annabawa. Me ya sa a ke zagin annabawa? Ba saboda sun zo da gaskiya ba ne? ko sun zo da karya ne? Ni zuciyata ba ta taba rudewa ko ta gigici ko na damu, don an zage ni ba, domin wanda ya zage ni din ya yi ne saboda a zatonsa na yi ba daidai ba. Ka ga shi alheri ya ke tunani, ni kuma na san ba kuskure na yi ba, daidai na yi. Don haka duk mu biyun mu na kan daidai. Kamar a filin kwallo ne; a na fara bol sai a ka zura kwallo a raga. To, ai wannan da a ka saka ma sa kwallo a raga, shi ma burinsa shi ne ya ci can. To, meye na rigima? Shi so ya ke ya bi Allah. Don haka ya ke ganin na saba. Don haka abin alheri ya yi, ni ma so na ke yi na bi Allah. Don haka na yi abinda ya ke daidai imanina, shi ma a imaninsa ya yi niyya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.