Dalilin Daya Sa Fim Din Mansoor Yayi Nasara – Inji Ali Nuhu

254Fitaccen jarumi kuma darakta, Ali Nuhu wanda aka fi sani da Sarki a masana’antar fim din Hausa ya bayyana cewa fim din Mansoor ya samu nasarar lashe gasa ce sakamakon yadda aka kokarta wajen nuna kwarewa a fim din.
Ali Nuhu ya bayyana haka ne bayan ya karbi kyautar karramawa a madadin kamfaninsa na FKD Production, wanda ya shirya fim din na Mansoor.
Shi dai fim din Mansoor ya lashe gasar fim da ya fi kayatarwa ne a cikin fina-finan cikin gida na Hausa a bikin The Africa Magic biewers’ Choice Awards na bana.
Da yake bayyana farin cikinsa a wajen taron, Ali Nuhu ya bayyana cewa fim din Mansoor kamar wani gwaji ne, kuma an samu nasara, “Ina sadaukar da wannan kyauta da muka samu zuwa ga wadanda suka taka rawa a fim din.
Musamman jaruman fim din da sauransu saboda yadda suka nuna min yarda da aminci a lokacin da muke shirya fim din. Fim din Mansoor kamar wani gwaji ne, amma kuma mun samu nasarar gwajin ya yi kyau. Na gode sosai.”
Ali Nuhu ya kara da cewa, “Ban taba amfani da fasahar zamani a fim ba kamar yadda muka gwada a fim din Mansoor. Don haka ban yi mamaki ba ganin yadda fim din ya samu wannan nasara.”

Comments are closed.