Dalilin da yasa ba mu kama masu bayar da wa’adin kabilar Ibo ba – Malami

102

Dalilin da yasa ba mu kama masu bayar da wa’adin kabilar Ibo ba – Malami Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin da ysa bata dauki mataki akan matasan Arewa da suka baiwa ‘yan kabilar Ibo wa’adin zama a yankunan Arewa ba A ranar Talata 29 ga watan Agusta, gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin da yasa ba ta kama kungiyar matasan Arewa ba bayan ta baiwa ‘yan kabilar Ibo mazauna wa’adin zama a yankunan zuwa ranar 1 ga watan Oktoba. Lauyan kolu kuma ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN) ne ya bayyana cewa, “bamu kama kungiyar arewa akan sanarwar wa’adin kabilar Ibo saboda wasu dalilai da suka shafi hakar tsaro da kuma zaman lafiya.” Malami ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da manema labarai a birnin tarayya.

Idan ba a manta ba, a kwanakin baya kadan, matasan Arewa sun baiwa ‘yan kabilar Ibo wa’adin zama a yankunan Arewa zuwa ranar 1 Oktoba.

Wanda a halin yanzu, matasan sun bayar da sanarwar janye wannan wa’adin a ranar Alhamis din makon da ya gabata. Kakakin wannan kungiya ta matasa, AbdulAziz Suleiman ya bayyana cewa, sun janye wa’adin sanadiyar tuntunbe-tuntube da wasu kungiyoyi daban-daban da suka samu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.