Dalilin Da Yasa Aka Daina Jin Duriyata A Masana’antar Kannywood – Adamu Nagudu

209

Adamu Hassan Nagudu fitaccen mawaki ne a masana’antar fina-finan Hausa. A shekarun bayan nan an daina jin duriyarsa, inda har wadansu suka fara tambayar ko ya daina harkar waka ce. A tattaunawarsa da Aminiya , mawakin ya bayyana dalilin da ya sa aka daina jin duriyarsa a harkar waka da dalilin da ya sa ya dawo harkar gadan-gadan yanzu da kuma shirinsa na ci gaba da fitowa a manyan fina-finai:

A ’yan shekarun da suka wuce an daina jin duriyarka, har wadansu sun fara tunanin ko ka daina harkar waka ce, yaya batun yake?
Nagudu: To, alhamdulillahi ka san ita harkar industiri da ma komai na duniya idan ka dauke shi a bisa sana’a, to, yana gaba ya kuma yi baya ne. Ko da kasuwanci ne samu yakan bambanta, za ka samu riba a wani lokaci, yayin da wani lokaci kuma faduwa ake kirgawa.

A harka ta industiri za ka ga yau wane a sama, ko wancan ne a sama, gobe kuma sai ka ga wance ko wane ne a kasa, haka abin yake juyawa. A da mawakan ma ba mu da yawa, amma yanzu ba zan ma iya kirga mawakan ba, mawaka a yanzu sun hada da yara da manya da ma sababbi.

Dalili na farko da ya sa aka daina jin duriyata shi ne, idan ka dubi yadda nake yin wakokina ba na sakin kundin wakoki na bidiyo ne ko na saurare a-kai-a-kai. Idan na yi albam nakan dauki shekara daya ko biyu kafin na sake sakin wani. A bana na kai shekara uku ko hudu ban saki wani kundin wakoki nawa ba, wannan dalili ne ya sa mutane suke tunanin na daina waka.
Dalili na biyu shi ne, yanayin kasuwa ta duniya ma komai a yanzu ya fadi, a shekarun bayan nan komai ya zama sai Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un. Kasuwancin ya taba ko’ina mu kanmu a yanzu ba za ka iya zuba kudinka, ka bata lokacinka ka yi waka ba, sannan ka kashe miliyoyin kudi wajen yin bidiyo ka sake a kasuwa amma ka fadi ba. Misali idan ka fitar da kwafi dubu 50, to kafin ka sayar da kwafi dubu biyar, to masu satar fasaha sun sayar da kwafi dubu 500, shi ya sa mutane suka ga a yanzu ba mu sake albam ba, yaya za mu sake bayan muna tsoron asara.
A yanzu zamani ya sauya inda yawancin mawaka suka koma kafar sadarwar intanet ta Youtube wajen sanya wakokinsu ko fina-finansu don a je a kalla, ko kai ma ka fara yunkurin haka?
A yanzu komai ya koma hanyar kafar sadarwar zamani, a yanzu maganar da nake da kai na saki wata sabuwar wakata wadda tun shekara uku zuwa hudu ban sake yin waka ba, sai wannan albam dina na yanzu, inda daya-bayan-daya zan rika sake su a Youtube mai suna Adamu Nagudu.
Ga wadanda ba sa shiga Youtube yaya za su yi su kalli wakokinka na yanzu ke nan?
Eh, sannu a hankali zan buga a faifan DBD don ya kai ga lungu da sako na kasar nan da wajenta.
Mene ne sunan albam din naka, sannan yana kunshe da wakoki kamar nawa?
Sunan albam din ‘Tauraro’, na kallo ne da na saurare, amma dai a Janairun sabuwar shekara zan fitar da shi a faifan DBD, wannan albam din zai fito da wakoki kamar shida.

Haka akwai wata waka da na yi inda na yi magana a kan ita kanta daukaka, a lokacin da Ubangiji (SWT) zai ba ka ita da kuma lokacin da zai karba. Albam ne da ya shafi kowa da kowa, akwai wa’azantarwa a ciki.

Comments are closed.