Dalilin Da Ya Sa Na Kori Malaman Firamare 22,000 – El Rufa’i

95


Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir ElRufa’i ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yanke shawarar korar Malam Makarantan Firamare 22,000 ne saboda duk da tsawon shekaru biyar da gwamnatin baya ta ba su na karo ilimi amma kuma har yanzu sun nuna rashin kwarewa kan harkar koyarwa bayan wata jarrabawa da aka yi masu wanda ya nuna kashi 25 sun fadi lissafi da tarihi.
A cikin jawabin da ya gabatar na sabuwar shekara, El Rufa’i ya nuna cewa a shekarar 2012, tsohon Gwamnan jihar, Marigayi Patrick Yakowa ya sallami malaman makaranta har 4000 saboda mallakar shaidar kammala karatu ta bogi inda kuma ya bayar da dama na shekaru biyar ga duk malamin da bai mallaki takardar shaidar koyarwa a cikin shekaru biyar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.