Dadin kowa sabon salo Episode 82 AREWA24

377

Madame Gloria ta riga ta gaji da ciyar da mijinta Daniel da ‘yarta Stephanie, ba don komai ba sai don ganin ‘yarta Stephanie ta ki amincewa da bukatarta ta auren Samule, wa tunaninta duk talaucin da suke ciki Stephanie ta janyo musu. A wani bangare daban, kawu Mala, gumu ta yi gumu, kansa ya dauki zafi domin rashin laifiyar ‘yarsa Bintu ta tsanananta ga babu kudin magani, wannan ce ta tilasta shi yin zabi tsakanin mummunan aski da sa kai a wuta, don haka sai ya nemi Daniel da ya samo masa mai sayen transformer wuta a boye. Daniel ya yi masa hanya zuwa wajen wani Inyamuri Onyebuci wanda ya sayi transformer a farashi mai rahusa.

Haka nan Dr. Amina ta ci gaba da bibiyar cin hancin da rashawar da ke kai kawo a makarantar su Bintu, inda ta dauki alwashin bayyana bara-gurbin malaman makarantar a duniy.

Download Here

Comments are closed.