BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA KUNGIYOYIN KARE HAKKIN MUSULMAI A NIGERIA

466

BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA KUNGIYOYIN KARE HAKKIN MUSULMAI A NIGERIA

Daga Datti Assalafy

Bayan rubutun da na wallafa akan wannann fitsararriyar mata wacce a da musulma ce amma yanzu tayi ridda kamar yadda ta bayyana, nayi kira ga dukkan jama’ar musulmi ta yadda za’a taimaka wajen dakile barnan da take yadawa a tsakanin al’ummar Musulmi Akwai wani babban mutum da ya kirani dazu da yamma yake fada min cewa na kyale wannan matar domin yarinyar wasu manyan mutane ne a Nigeria suna harka da ita, duk wanda yayi yunkurin taka mata burki to kamar ya taro wani babban bala’i ne To amma abin tambaya anan shine; wai shin haka al’ummar Musulmi zata zama?

don ana jin tsoron wane saboda matsayinsa ana tafka barna amma ba za’a fadi gaskiya a gyara ba saboda tsoron abinda zai biyo baya?

wannan abin takaici ne Ina amfani da wannan damar wajen yin kira ga dukkan Kungiyoyin kare hakkin Musulmi a Nigeria, da Mai Alfarma Sarkin Musulmi da majalisarsa na manyan Sarakunan Musulunci da kuma manyan Malamai, tunda ance takalar wannan matar daidai yake da takalar wasu manyan mutane a Nigeria to ya kamata fadan ya koma na manya Dole ne shugabannin Musulmai suyi bincike sosai a kanta, abi dukkan matakai da ya dace wajen dakile barnar da take yadawa a tsakanin al’ummar musulmai Yaa Allah Mun kawo karar wannan matar zuwa gareKa, babu wayo babu dabara sai naKa Yaa Allah Ka nufeta da shiriya, idan ba zata shiryu ba Allah Ka lalata dukkan mugun nufinta, Ka toshe mata duk wata hanya da take amfani dashi wajen halakar da al’ummah Amin

Leave A Reply

Your email address will not be published.