BABU BAMBANCIN TSAKANIN DAN ZINA DA DAN HALAL A WAJAN RABON GADO

239

*BABU BAMBANCIN TSAKANIN DAN ZINA DA DAN HALAL A WAJAN RABON GADO

*Tambaya*

Assalamualaikum dan Allah tambaya nake yi mu biyar mamanmu ta haifa amma biyu daga cikinmu ta hanyan aure aka same su uku kuma ba tahanyar aure aka same su ba, shin sunada gadon ta ko, ba su ? kuma ta mutu da bashi da yawa akanta kuma ba mu da hanyar biya mata shi domin kudin suna da yawa akalla yakai dubu dari biyu.

Dan Allah mafita muke nema, Mungode

*Amsa*

Wa alaikum assalam, idan mace ta yi cikin shege kuma ta haifi Da, daga baya ta mutu Dan zinar da ta haifa zai gaje ta, saboda Allah madaukakin sarki a cikin suratun Nisa’i aya ta : 10 ya yi wasiyya a bawa ‘ya’yaye gado, Dan zina kuma yana cikin jerin ‘ya’yayen mahaifiyarsa, wannan yasa zai gaje ta.

Don haka babu Bambanci a cikinku tsakanin Wanda aka haifa ta hanyar aure da kuma Wanda aka samu ta hanyar Zina.

Ba’a raba gado sai an fara biyawa mamaci bashinsa, don haka ko da duk abin da ta bari zai kare dole Ku biya kafin a raba, kamar yadda Allah ya bayyana a cikin suratun Nisa’i aya ta (11).

Dan zina baya gadon mahaifinsa ko da kuwa mahaifin ya amince Dansa ne a wajan mafi yawan malamai.

Allah ne mafi sani.

*Dr. Jamilu Zarewa*

03/11/2018

Comments are closed.