Babban basarake a Arewa ya yabawa kokarin gwamnati wajen magance Boko Haram

193


A yau, Talata ne Mai Martaba Sakin Dutse, Dr Nuhu Sunusi ya yabawa gwamnatin tarayya kan namijin kokarin da ta keyi wajen magance ta’addancin kungiyar Boko Haram. Sarkin ya yi wannan jawabin ne a fadarsa da ke Dutse a jihar Jigawa yayin da ya karbi bakuncin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo. Ya ce idan akayi la’akari da yadda al’umma ke kiyasin ayyukan gwamnati, za a iya cewa gwamnatin Shugaba Buhari ta mayar da hankali sosai wajen yaki da ‘yan ta’addan da kawo karshen hare-haren da su keyi.
Babban basarake a Arewa ya yabawa kokarin gwamnati wajen magance Boko Haram “Kunyi kokari wajen yaki da ‘yan ta’addan kuma mun ga banbanci. “Hankulan mutane ya kwanta yanzu idan aka kwatanta yadda suke rayuwa a baya,” inji shi.
Da farko, mataimakin shugaban kasar ya ce ya kai ziyara fadan sarkin ne domin ya sanar dashi wasu shirye-shiryen gwamnatin tarayya na inganta rayuwar talakawan Najeriya.

Osinbajo ya ce gwamnatin tarayya ta bullo da shirye-shirye da dama karkashin Special Intervention Programme (SIP) domin inganta rayuwar al’ummar Najeriya musamman masu karamin karfi da mata. Ya ce shirye-shiryen sun hada da Tradermoni, N-Power, Shirin ciyar da daliban makarantun frimari da Conditional Cash Transfer (CCT). “Burin mu shine kawo sauyi a rayuwan kowanne ‘dan Najeriya musamman kananan ‘yan kasuwa da talakawa saboda sune suka fi yawa cikin al’umma. “Kuma muna fatan zamu inganta rayuwar al’ummar Najeriya,” inji Osinbajo. NAN ta ruwaito cewar mataimakin shugaban kasan ya ziyarci jihar ne domin kaddamar da shirin bayar da tallafi na gwamnatin jihar da na tarayya.

Comments are closed.