Ba Na Jin Tsoron Muhammad Salah —Sergio Ramos

180Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Sergio Ramos, ya bayyana cewa baya tsoron haduwa da dan wasan gaba na Liberpool Muhammad Salah a wasan karshe da zasu fafata na cin kofin zakarun turai a karshen wannan watan.

Ramos ya bayyana hakane a wata hira da yayi da manema labarai inda yace babu abin tsoro a wajen Salah kawai yana daukar dan wasan daya daga cikin yan wasa 11 da zasu bugawa Liberpool.

Yace ya hadu da manya manyan shahararrun yan kwallo a duniya wadanda ake tunanin babu kamarsu a duniya kuma baiji tsoronsu ba saboda tsoro baya daya daga cikin halin dan wasan baya.

Yaci gaba da cewa Salah kwararren dan wasa ne kuma yaga abinda yabuga a wannan kakar amma maganar tsoro babu ita kawai dai yana girmama shi kamar yadda yake girmama ragowar yan kwallo a duniya.

Ya kara da cewa akwai yan kwallo masu hazaka da kokari daya fuskanta a rayuwarsa ta kwallon kafa kuma ya girmama su saboda yadda suka ajiye tarihi kuma suke buga kwallo sosai amma bai taba jin tsoron kowanne dan wasa ba.
Salah dai ya kasance jagoran kungiyar kwallon kafa ta Liberpool bayan daya jagoranci kungiyar zuwa wasan na karshe sannan kuma ya zura kwallaye 43 cikin wasanni 48 daya buga a wannan kakar kwallaye 9 a gasar zakarun turai yayinda yaci 31 kuma a gasar firimiya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.