An yi garkuwa da gawa don neman kudin fansa

121'Yan sanda sun kama mutum biyu da ake zargi da garkuwa da gawar wata tsohuwa a kudu maso-gabashin Najeriya.

'Yan sanda daga Oweri, babban birnin jihar Imo, sun ce mutanen sun sace gawar ne daga wajen ajiye gawa a wani asibiti, kuma suka kai ta daji suna masu neman naira miliyan hudu a matsayin kudin fansa daga asibiti da kuma iyalan marigayiyar, in ji 'yan sanda.
An kama wadanda ake zargin, wadanda a baya aka taba samu da laifi, a wani samamen da aka kai musu.

Tuni dai akai mayar da gawar ga iyalan marigayiyar.


Kwanan nan aka sako mutanen daga gidan yari bayan sun yi zaman kaso bisa laifin garkuwa da mutane.

©BBCHAUSA

Leave A Reply

Your email address will not be published.