An sako tagwayen da aka sace a Zamfara

229

Masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara sun sako ‘yan matan nan tagwaye da suka sace a watan jiya.
Dangin tagwayen da kuma wani babban jami’i a Karamar Hukumar Zurmi daga inda aka dauke su, sun tabbatar wa BBC da sakin nasu.
Kuma sun ce suna cikin koshin lafiya.
Sai dai kuma sun ce ba a sako yayarsu ba – wacce aka kama su tare a wani gida da ke garin Dauran a watan jiya a yayin da suka je rabon katin bikin aurensu.
Karin bayani game da Zamfara:
Kashi 67.5 ke rayuwa cikin talauci
Iya karatu da rubutu: Kashi 54.7
Take: Noma tushen arzikinmu
Yawancin mutanen jihar manoma ne daga Hausa Fulani
Yawan jama’a: Miliyan hudu da rabi (Alkalumman shekarar 2016)
Musulmi ne mafi yawa
Jihar da aka fara kaddamar da Shari’a – a 2000
Madogara: Shafin alkalumma na Najeriya.
Karanta karin wasu labarai masu alaka:
An yi garkuwa da mutane da dama a Zamfara
Me ya sa babu wanda ya damu da rikicin Zamfara?

Comments are closed.