An Kama Wasu Maza Biyu a Yayin Da Suke Yunkurin Binne Asiri

316

Rundunar ‘yan sandan jahar Kwara ta gurfanar da wasu maza biyu, Abdullahi Adebayo da Suleiman Olanrewaju a gaban kuliya bayan da aka kama su na yunkurin binne asiri a wani gidan da ake kan ginawa.

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya NAN ya rahoto cewa yan sandan na tuhumar Adebayo mai shekaru 38 da Olanrewaju mai shekaru 39 da laifin hada baki wajen aikata mummunan laifi da kuma rike asirin da ake amfani da shi wajen aikata laifi.

Dan sanda mai kara, insfekta Zacheous Folorunsho ya fadawa kotun cewa a ranar 5 ga watan Disemba ne wani mai suna Mohammad Abdulrahman wanda shine mamalakin ginin da suka yi yunkurin binne asirin ya kai karar lamarin ofishin ‘yan sanda.

Alkalin kotun, Abdulrahman Bello ya bada belin mutanen biyu akan Naira dubu 50 kowannensu.

An daga sauraran karar zuwa ranar 11 ga watan Janairu.

Comments are closed.