An Gargame Wani Manomi A Kan Zargin Yiwa Wata ‘Yar Shekaru 12 Fyade

164


Wata kotun Majistare da ke Kano a ranar Alhamis ta yankewa wani manomi dan shekaru 67, Lawan Umar, hukuncin daurin shekaru 7 a gidan yatri bayan ta kama shi da laifin yiwa wata yarinya ‘yar shekaru 12 fyade.
Wanda aka yankewa hukuncin na zama a kauyen Garindau wanda ke karamin hukumar Warawa a jihar Kano, an caji shi da aikata babban laifin lalata.
Karanta wannan: Ta Sa Hakora Ta Gatsa Mazakuntar Matashin Da Ke Yunkurin Yi Ma Ta Fyade Lauyan da ya mika karar zuwa kotu, Sajan Shehu Adam, ya bayyanawa kotun cewa wani mai mutum mai suna Bilyaminu Ahmed daga kauyen Garindau ya kai rahoton fyade zuwa ofishin ‘yan sanda da ke karamar hukumar Warawa a 14 ga watan Mayu 2017.
Karanta wannan: Tirr! Ango Ya Yiwa ‘Yar Shekaru 6 Fyade
Ahmed ya bayyana cewa a wannan ranar a misalin karfe 9:00 na safe, wanda ake zargi ya yiwa yarinyar wayo a yayin da ta ke hanyar zuwa Islamiyya zuwa dakin sa da ke kauyen wurin da ya ma ta fyade.
“Wanda ake zargi yayi lalata da yarinyar ta hanyar amfani da iya karfensa, har sai da ya yi ma ta rauni.”
Karanta wannan: Yadda Wani Mutum Ya Yi Wa Abokiyar Aikin Shi Fyade Bayan Ya Barbada Wiwi a Abincin ta
Raunin da wadanda ake zargi ya yiwa yarinyar ya sa har sai da aka garzaya da ita zuwa asibitin Warawa don duba lafiyarta tare da yi ma ta magani.
Laifin ya sa sabawa sashe 285 na dokar Panel Code.
Karanta wannan: Uba Da Kanin Shi Sun Yi Wa ‘Yar Su Mai Shekaru 16 Fyade
Umar ya furta aikata laifin da ake zarginsa da shi inda ya roki kotun ta gafarta masa. Alkalin kotun, Majistare Maryam Sabo, ta yankewa Umar hukuncin daurin shekaru 5 ba tareda biyan kudin fansa ba tare da karin wasu shekaru 2 ko kuma ya biya diyyar naira N50,000 a kan aikata babban laifin lalata.

Leave A Reply

Your email address will not be published.