An gano kabarin wani malami na zamanin ‘fir’auna’

315
‘Yan jarida sun samu daman shiga cikin hubbaren da ke Saqqara mai nisan kilomita 30 da birnin Alkahira na Masar

Masar ta gano hubbaren wani babban jagoran addinin wanda ya kai shekaru kusan dubu hudu da dari biyar da mutuwa.

An dai gano hubbaren ne a daya daga cikin katafaren yankin Saqqara da ake da dalar Masar irin ta zamanin da.

Ma’aikatar adana kayayyakin tarihi ta masar ta ce hubbaren na wani babban malamin addini ne na gidan sarauta da iyalansa a lokacin daula ta biyar ta mulkin fir’aunan.

Bangon hubbaren na dauke da zane mutum-mutumin mutanen gidan da kuma wasu zane-zane na kawa da ke nuna irin wasu ayyukan da sukeyi kamar tuka jirgin ruwa, farautar tsunbtsaye da hadaya.

Sakatare janar na majalisar koli da ke kula da kayyakin tarihi na kasar ta Masar, Dokta Mostafa Al-Waziri, ya ce a hubbaren akwai wasu sako-sako wanda ke nuna cewa akwai alamomin wasu tarin kayayanki tarihi adane acikinsa.

A wannan lahadin dai ake shirin soma aikin tono hubbaren wanda ake saran a sake gano wasu abubuwa tarihi da dama a ciki.

Ga abubuwan da aka gano…


An dai gano hubbaren ne a daya daga cikin katafaren yankin Saqqara da ake da dalar Masar irin ta zamanin da


An gano hubbaren a karkashin wani tsauni, wanda watakil hanya ce a wancan zamani ta tserewa


Bangon hubbaren na dauke da zane mutum-mutumin mutanen gidan da kuma wasu zane-zane na kawa


Mutanen da kan yi zane-zane mutum-mutumi a bango hubbaren da wurin bauta

Mostafa Al-Waziri, wanda ke jagoranta tono abubuwan da ke kunshe a hubbaren ya ce hubbaren ya kai tsayin mita 10, fadinsa kuma mita 3 ne haka kuma zurfinsa

Malaman addinin na da muhimmanci sosai kuma sun yi tasiri ga mutanen da a Masar


Hubbaren na dauke da zane-zanen da aka yi shekaru 4,400 a cewar masana


Tun zamanin sarki Neferirkare Kakai aka yi wannan mutum-mutumin lokacin daula ta biyar ta mulkin fir’aunan

Zane na nuna irin wasu ayyukan da babban malamin adinin da iyalansa ke yi


Masu bincike na saran wannan sako zai kai su ga akwatin gawar babban mutumin da aka bine a wannan hubbare

@BBCHAUSA

Comments are closed.