An Fara Bikin Jarumar Bollywood, Priyanka Chopra

272

A yau, 29 ga watan Nuwamba ne aka fara bikin shahararriyar jarumar Bollywood, Priyanka Chopra da mawaki dan kasar Amurka, Nick Jonas.

Bikin wanda za a shafe kwanaki biyar ana yi zai kankama ne daga a ranar biyu ga watan Disamba.

Masoyan junan za su yi biki nau’i biyu, wato da na al’adar Hindu, wanda shi za a fara, sai kuma biki irin na kiristanci da za a yi washegari.

Jama’a da dama dai sun dade suna jiran zuwan wannan kasaitaccen biki.

An kiyasce cewa za a kashe kwatankwacin dala miliyan 60 wajen gudanar da bikin.

Comments are closed.