An Dakile Kokarin Safarar ‘Yan Mata 8 Daga Ghana A Filin Jirgin Sama Na Legas

125

Jami’an shige da fice ta Nijeriya sun dakile kokarin safarar ‘yan mata guda 8, a filin jirgin Murtala Muhammed dake jihar Legas. An dai cafke wadanda ake zargi ne ranar Litinin a filin jirgin na jihar Legas, lokacin da suke kokarin zuwa kasar Kuwait inda daga nan sai su shiga kasar Libya sannan kuma sai su yi kasar Turai da su. Jami’an shige da ficen sun dai samu nasarar cafke wadanda ake zargi ne lokacin da suka binciki wata yarinya, sannan suka same ta da fasfo din kasar Ghana kuma ita ‘yar Nijeriya ce. An dai bayyana wa jami’an cewa ‘yan matan masu shekaru 20 zuwa 25 suna so daga Nijeriya sai su shiga kasar Turai. Majiyarmu ta tabbatar da cewa ‘yan matan sun fito ne daga kasar Togo da kuma kasar jamhuriyar Benin bisa tallafawar wadanda suka taimaka masu. A cewar majiyarmu,‘yan matan ba su da wata dalilin yin amfani da kasar Nijeriya zuwa kasar Turai. Majiyar ta kara da cewa,“lamarin ya janyo hayaniya da jami’an. Lokacin da aka tambaye su, sai suka yi ikirarin cewa su masu gaskiya ne kuma za su je kasar Turai ne, amma za su fara sauka a kasar Kuwait. Lokacin da aka bincika sai aka samu cewa, ‘yan matan sun shigo Nijeriya ne ta hanyar mota daga kasar Ghana, inda suka shiga kasar Togo sannan suka zarce zuwa kasar jamhuriyar Benin.
“Wannan ba shi ne karo na farko wanda muka dakele safarar mutane a filin jirgi ba, sannan kuma rundunarmu za ta ci gaba da kula wa domin mu tabbatar da cewa mun dakele wannan mummunar lamarin.”
Jami’in hudda da jama’a na hukumar shige da fice Sunday James ya tabbatar da faruwar lamarin.
“Rundunar tamu samu nasarar cafke mata guda 8 ‘yan asalin kasar Ghana, za mu mika su ga hukumar dake yaki da safarar mutane ta kasa domin gudanar da cikikkyan bincike,” inji shi.

@HausaLeadership

Leave A Reply

Your email address will not be published.