An Ci Zarafin Yara Mata Fiye Da 500 Cikin Watanni 10 a Kano – Lauya

203

Wata lauya a jahar Kano, Barista Maryam Ahmed Sabo ta ce cin zarafin mata da kananan yara ya yi kamari a cikin al’ummar Nijeriya.

Da ta ke magana da kafar yada labarai na BBC, baristar ta ce an kiyasce cewa a cikin mata 10 a kan samu uku da aka ci zarafinsu ta hanyoyi daban-daban.

Ta ci gaba da cewa, ba ta hanyar fyade kadai ake cin zarafin mata ba, akwai wasu hanyoyin daban kamar yi musu kaciya ko kuma fadan cikin gida.

Lauyar ta ce lamarin ya fi kamari a jahohin Lagos da Kano da kuma jahar Borno, duk da cewa akan samu aukuwarshi a ko’ina a fadin kasar nan.

Haka zalika ta ce daga wata daya zuwa shekaru 14 na ‘ya mace ne ta fi fuskantar barazanar wannan matsala.

A cewarta, “A jahar Kano kadai, tsakanin farkon shekarar 2018 zuwa watan Oktoba, an ci zarafin yara fiye da 500’.

Daga cikin matsalolin da ke haifar da matsalar, barista Maryam ta ce akwai sakaci na iyaye da na masu bayar da tarbiyya, akwai rashin jin tsoron Allah, akwai tallace-tallacen da ‘ya’ya mata ke yi da auren dole.

Comments are closed.