An Bawa Nura M Inuwa Kyautar Makudan Kudade

1,166

A makon da ya gabata ne dai jami’ar Maryam Abacha American University Niger (MAAUN) tayi bikin yaye dalibanta karo na biyu a birnin Maradi dake kasar ta Nijar.

An gayyaci mawaki Nura M Inuwa don ya nishadantar dasu da wakokin sa masu dadi wanda bayan kammala taron ne aka bashi kyautar tsabar kudi har naira milliyan biyu(N2 million) sannan kuma aka bashi takardar gurbin yin karatu a makarantar.

Alhamdulillah Godiya ta tabbata ga ALLAH S.W.T daya nuna mana ranar da Maryam Abacha American University (MAAUN) ta yaye dalibanta karo na biyu.Tabbas wannan wata nasarace kuma wani cigabane ga Kasata Nigeria, Niger, Africa dama duniya baki daya.

Ina kara amfani da wannan dama wajen yin godiya ga hukumar makarantar baki daya ,musamman Prof. Adamu Abubakar Gwarzo (Shugaban makaranta) kamar yadda Kuka sani shekarar da ta gabata ya bani mota, a wannan karon kuma ya bani kudi naira million biyu 2,000 000, Ina masa addu’ar Allah ya kara yalwata arzikinsa Ina mika godiya ga Dr. Bala Muhammad, Da Muhammad Adamu wakili, dangane da kauna da soyayyar da suke nunawa a gareni.

Sannan ina mai farin cikin shedawa hukumar makarantar cewa ni Nura M Inuwa nayi farin ciki da Admission din da suka bani domin yin nazari a karkashin inuwar Maryam Abacha American University (MAAUN).

Ina kara godiya da fatan alkhairi ga Prof. Adamu Abubakar Gwarzo Allah ya kara aziki,rufin asiri da wadata ya kuma sa kuyi kyakkyawan karshe,Sannan Allah ya kara daukaka Maryam Abacha American university (MAUUN), kuma Allah ya tsareku duk wani sharri da duk wani abun qi.

Sannan ina rokon masoyana dasu tayani addu’a da godiya ga wannan hukumar makaranta mai albarka (MAAUN).
Nagode! Nagode!! Nagode!!

@arewamobile

Comments are closed.