Allah Ya Yiwa Shahararren Dan Wasan Kwaikwayon Nollywood Elder Danda Rasuwa

197

Allah ya yiwa Shahararren dan wasan kwaikwayon Nollywood, Elder Ifeanyi Ikenga Gbulie, rasuwa.

Mamacin wanda aka fi sani da suna, Elder Danda, ya rasuwa kwanaki 2 da suka gabata bayan ya ta fama da ciwon cutar shanyewa jiki (stroke). Ifeanyi ya rasu ne a birnin Enugu

Daraktan Guild of Nigeria, DGN, Chima Okoroji, ya tabbatarwa manema labarai dan rasuwar marigayin.

“Abun yayi matukar ratsa ni; Ina matukar son wannan mutumin. Zan ji kewarsa sosai” ya ce.

An fi sanin dan wasan kwaikwayon a fim din da ya fito mai suna End of Dreams and Under Fire

Leave A Reply

Your email address will not be published.