Ali Nuhu da Rara sun halarci kaddamar da kamfen din gwamnan APC a arewa

874


Ali Nuhu da Rara sun halarci kaddamar da kamfen din gwamnan APC a arewa
A ranar, Litinin, ne gwamnan jihar Adamawa, Jibrilla Bindow, ya kaddamar da yakin neman zabensa
Yakin neman zaben da aka kaddamar a Ribadu Square ya samu halartar manyan ‘yan siyasar jihar Adamawa – Gwamna Bindow na fuskantar adawa mai karfi daga cikin jam’iyyar APC bisa zarginsa cogen takardun karatu Sati biyu bayan ‘yan takarar gwamnan a jam’iyyun PDP, Umaru Fintiri, da SDP, Emmanuel Bello, sun kaddamar da yakin neman zabensu, gwamna Jibrilla Bindow na jihar Adamawa ya kaddamar da nasa kamfen din a jiya, Litinin.

Yakin neman zaben da aka kaddamar a Ribadu Square dake Jimeta a garin Yola ta samu halartar manyan jaruman masana’antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood). Fitattu daga jaruman Kannywood da suka halarci sun hada da Ali Nuhu da Dauda Kahutu Rara.
Ana kyautata zaton Bindow zai lashe zaben gwamnan Adamawa cikin sauki bisa dogaro da farin jinin da yake da shi a jihar saboda aiyukan da ya yiwa jama’a. Sai dai har yanzu Bindow na fuskantar adawa daga cikin jam’iyyar APC a wurin abokan takarar sa, Nuhu Ribadu da Ahmed Halilu (Modi) da suka fafata a zaben fidda ‘yan takara da aka yi a watan Oktoba na shekarar da ta kare.

Ribadu da Modi na zargin saba dokokin jam’iyya a zaben da ya samar da Bindow a matsayin dan takarar gwamna a karo na biyu. Duk da adawar da Bindow ke fuskanta daga manyan ‘yan siyasar biyu, masu alhakin yi masa yakin neman zaben na ganin cewar hakan ba zai hana shi samun nasara a zaben da za a yi a watan Fabrairu mai zuwa.

@NaijHausa

Comments are closed.