Ali Nuhu da jerin fitattun jarumai da su ka taya Buhari murna

461

Wasu daga ciki fitattun jaruman masana’antun nishadantarwa sun yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari muranar sake lashe zabe a karo na biyu.

Fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa, Ali Nuhu, ya bayyana jin dadin sa tare da taya shugaba Buhari murnar sake lashe zaben shugaban kasa.

“ Jinjina ga shugaba na PMB! Ina taya dukkan masoya Buhari murna, mun yi nasara duk da irin batanci da zolayar da ake mana.

Mu na godiya ga Allah ,” kamar yadda jarumin ya rubuta. Jaruman sun bayyana gamsuwar su da yadda zabe ya gudana da nuna jin dadin su da nasarar da shugaba Buhari ya samu.

Wata jaruma, Joke Silva, ta rubuta a sahfin ta na Tuwita (@ajokesilva), “i na taya shugaba Buhari murna. Ka yi rawar gani. “Shekaru hudu ba wani lokaci ne mai tsawo ba.

Allah y aba ka ikon yin amfani da damar da ka samu, ya kuma kara ma ka kaifin basira .”

Shi kuwa jarumi kuma dan siyasa, Desmond Elliot, wanda dan majalisar dokokin jihar Legas ne ya bayyana jin dadin sa.

Ya rubuta sakon sa kamar haka, “ ina taya shugaba Buhari murna.

Tazarcen Buhari zai kawo dorewar aiyukan gina Najeriya da shugaban kasa ya fara dasa tubulin su a zangon san a farko.

“Ina taya shugaban kasa Murna, ina taya jam’iyyar APC murna, ina taya ‘yan Najeriya murna .

Kazalika, shi ma jarumin masana’antar Kannywood, Adam A. Zango, ya taya Buhari murnar samun nasara.

Ana daf da shiga jajiberin zabe ne Zango ya yi mi’ara koma baya, ya dawo goyon bayan shugaba Buhari bayan a kwanakin baya an bayyana cewar ya koma bayan Atiku Abubakar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.