ABUBUWAN DA AKE SO MACE TA FI MIJINTA DA SU-Dr Zarewa

230

ABUBUWAN DA AKE SO MACE TA FI MIJINTA DA SU

Tambaya :
Aslkm, malam ya azumi dafatan kasha ruwa lafiya.WASU TAMBAYOYI NAKE ROKON Malam daya taimakamin da amsoshinsu in Allah yasa malam yasansu.1.SHIN MALAM Wai a kwai wasu abubuwa uku da ake so mata tafi mijin da zata aura dasu,sannan shima akwai abu guda uku da’akeso yafita dasu?,sannan akwai wadanda sukayi musharaka akansu,DAFATAN MALAM YASANSU KUMA ZA’A TAIMAKAMIN DA Su.NAGODE

Amsa :
To dan’unwa masana ilimin zamantakewar aure suna cewa, ana so mace ta fi mijinta da abubuwa uku : ta fi shi a kyau, ta fi shi kananan shekaru, ta fi son shi, sama da yadda yake sonta .
Ana so miji ya fi matarsa da abubuwa uku : ya fi ta kudi, ya fi ta ilimi, ya fi ta jarunta
Ana so su hadu a abubuwa uku : ya zama akwai yaran da yake hada su, ya zama addininsu daya, ya zama dukkansu suna son tarbiyya.
Idan aka samu wadannan uku-ukun, to za’a samu jin dadin aure.

DON NEMAN KARIN BAYANI KA NEMI SHIRIN DA NA YI A FREEDOM RADIO KANO, RANAR : 3 GA RAMADHAN 1434 HI, A SHIRINSU NA MINBARIN MALAMAI

Comments are closed.