Abin tausayi: Kuji irin maganganu masu ratsa zuciya da Nafisa Abdullahi ta dinga yi akan gawar mahaifiyarta

133Mahaifiyar fitacciyar jarumar shirin fim din Hausan nan wacce aka fi sani da Nafisa Abdullahi ta rasu


- Jarumar tace har yanzu ta kasa gaskata rasuwar Mahaifiyar tata

- Ta rasu a ranar Talata bayan fama da jinya da tayiAllah yayiwa mahaifiyar daya daga cikin jaruman Hausa fim Nafisa Abdullahi ta rasuwa.

Mahaifiyar Nafisa ta rasu a ranar Talata a Abuja bayan fama da jinya.

Jarumar tace har yanzu ta kasa gaskata rasuwar "Ina ma ace mafarki nakeyi wani yazo ya tasheni, amma ido biyu ne. Mahaifiya ta ta rasu."

Jarumar wadda akafi sani da 'Nafisa Sai Wata Rana' ta bayyana cewa mahaifiyarta ta horeta data zama jajirtacciya a halin rayuwa.

Tace "Na taba fuskar ki, kafarki da kuma hannun ki ina tunanin kozaki tashi amma baki tashi ba, nasan kema bakiso kika tafi kika barmu ba amma ya zama dole tunda lokacin ki yayi, har yanzu ina ganin murmushin da yake kan fuskar".

Har yanzu ina ganinki kina kallo na, amma bakice komai ba, kinci gaba da kallo na na tambaye ko kina bukatar wani abu amma bakice komai ba, ina ma nasan abunda yake cikin zuciyar ki, da kuma abinda kikeson sanar dani.

Leave A Reply

Your email address will not be published.